Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyo: Da kake ta zagin ‘yan Fim, Toh matarka kawarmu ce, maza da matan mu ‘yan Fim kawayen matarka ne kuma mun ci Arzikin Juna>>MC Ibrahim Sharukhan ya mayarwa da Sheikh Lawal Triumph martani bayan da ya caccaki ‘yan Fim

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Tauraron fina-finan Hausa kuma MC Ibrahim Sharukhan Ya mayarwa da malamin Addinin Islama, Sheikh Lawal Triumph martani kan sukar ‘yan fim.

Da farko dai Tijjani Faraga ne ya bayyana cewa, Shi ba dan Iazala bane kuma duk wanda ya kara hadashi da Izala Allah ya isa.

Daga nan kuma sai Malam Lawal Triumph ya mayar masa da martanin cewa ai babu ‘yan fim da ‘yan Daudu, da Bokaye a Izala.

A martanin MC Ibrahim Sharukhan yace malam da yake zagin ‘yan Fim ya sani matarsa Allah ne kawai yayi ba zata yi fim ba amma tana da kawaye maza da mata ‘yan fim.

Karanta Wannan  Wani Malamin Addinin Islama daga kasar Yarbawa ya dauki hankula bayan da yace wai idan ka gayawa Saniya cewa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi Wafati zaka ga Bàlà'i, ba zaka koma gida Lafiya ba

Lamarin dai ya dauki hankula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *