
Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Najeriya na nan rike da alkawarin Haramta gwajin makamin kare dangi.
Yace abinda ke gaban Africa a yanzu shine magance matsalar talauci canjin Yanayi, ba maganar mallakar makamin kare dangi ba.
Shugaban ya bayyana hakane yayin ganawa da shugaban kungiyar hana gwajin makamashi ta Duniya, Dr Robert Floyd.
Dr Robert Floyd da tawagarsa sun gana da Kashim Shettima ne a ofishinsa dake Abuja.