
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya koka da cewa, makiya nason kifar da Gwamnatinsa.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga inda yace Dama tun kamin shugaban ya karbi Mulki, Sarki Sanusi II ya fada cewa Gyare-Gyaren Tinubu ba zasu zo da sauki ba.
Onanuga yace amma duk da masaniyar wannan, Makiya na kokarin kifar da gwamnatin Tinubu wadda ke kokarin gyara kasarnan.