
A yau, Talata ne majalisar Dattijai ta Jibge jami’an tsaro dan hana sanata Natasha Akpoti komawa majalisar.
Hakan na zuwane duk da umarnin da kotu ta bayar na cewa a janye dakatarwar da akawa sanata Natasha Akpotin.
Saidai majalisar tacw sai ta yi zama na musamman akan lamarin.
An dai dakatar da sanata Natasha Akpoti ne saboda zargin kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio da nemanta da lalata da kuma take dokokin majalisar.