
Malam ya bayyana cewa fadan Hujja da Littafi ne ‘yan Darika ba zasu iya ba shiyasa suka koma neman fadan zahiri.
Ya bayyana hakane a Bidiyo sa da yake mayar da martani kan masu sukar Sheikh Lawal Triumph.
Lamarin ya samo Asaline daga hadisan da Sheikh Lawal Triumph ya karanto dake cewa, An samu Kwarkwata akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da wanda ke cewa, Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) na fitsari a tsaye.
Malamin yace ‘yan Darika na zuga gwamnatin Kano ta kama Sheikh Lawal Triumph saidai yace fada da malamin gaskiya ba riba.