Monday, December 16
Shadow

Me ke janyo ciwon baya: Maganin ciwon baya mai tsanani

Ciwon baya na iya samun babba ko yaro, sannan yana iya samuwa a kasan baya, wajan kugu, ko kuma a saman baya.

Akwai dalilai da dama dake kawo ciwon baya wadanda zamu zayyano a kasa:

  • Jin ciwo na zahiri
  • Daga wani Abu ba yanda ya kamata ba.
  • Daga wani abu me nauyi sosai.
  • Motsi ba daidai ba.
  • Ciwon gabobi wanda tsuwa ke kawowa.
  • Tari ko Atishawa.
  • Yin mika ba daidai ba.
  • Dukawa ta tsawon lokaci.
  • Turawa, jaa, ko daukar wani abu.
  • Zama ko tsayuwa na tsawon lokaci.
  • Yin tuki na tsawon lokaci.
  • Kwanciya akan katifar da bata dace da jikinka ba.
  • Akwai ciwon dajin dake kawo ciwon baya.

Su wanene ciwon baya yafi kamawa?

Akwai mutanen da yanayin da suke ciki ko kuma irin abubuwan da suke yi ke sa sufi zama cikin hadarin kamuwa da ciwon baya.

Irin wadannan mutane sune:

  • Mace me ciki.
  • Yawan zama ba tare da motsa jiki ba.
  • Tsaffi.
  • Wadanda kiba tawa yawa.
  • Masu shan taba, sigari.
  • Yawan motsa jiki babu hutu, musamman idan aka yi ba bisa ka’ida ba.
  • Ana gadon ciwon baya.
  • Yawan bacin rai na kawo ciwon baya.
  • Mata sun fi kamuwa da ciwon baya ta can kasa fiye da maza.
Karanta Wannan  Ganyen gwaiba na maganin infection

Alamun da idan mutum ya ji a jikinshi ke nuna cewa yana fama da ciwon baya:

  • Rama
  • Zazzabi
  • Kumburar baya.
  • Ciwon baya wanda ko an zauna ko an huta baya sauki.
  • Ciwon kafa.
  • Ciwon gwiwa.
  • Kasa rike fitsari.
  • Wahala wajan yin fitsari.
  • Wahala wajan yin kashi.
  • Jin kamar al’aurarka ba a jikinka take ba.
  • Jin kamar duburarka ba a jikinka take ba.
  • Jin kamar mazaunanka ba a jikinka suke ba

Yaushe ya kamata a ga Likita?

Ya kamata a gaggauta zuwa Asibiti idan aka ji daya daga cikin abubuwan da zamu zayyano a kasa ga mai ciwon baya:

  • Idan ciwon baya yaki sauki duk da cewa ana samun hutu da nutsuwa.
  • Idan aka fara jin ciwon baya bayan faduwa ko kuma bayan jin ciwo na zahiri.
  • Idan mutum ya fara jin kafafuwansa kamar basa jikinsa.
  • Idan mutum ya ji kasala ta mai yawa.
  • Jin Zazzabi.
  • Rama.
Karanta Wannan  Maganin istimna'i na gargajiya

Maganin ciwon baya na gargajiya

Akwai hanyoyin da ake bi wajan magance matsalar ciwon baya a gargajiyance wanda kuma har likitoci sun amince da hakan.

Wadannan hanyoyi sun hada da:

  • Shan magungunan ciwon jiki irin su ibuprofen.
  • Dora wani abu me zafin da ba zai cutar ba akan inda ake jin ciwon.
  • Dora jaka ko ledar kankara a kan inda ake jin ciwon.
  • Rage yawan ayyukan karfi, amma kuma adan rika motsa jiki na taimakawa.
  • Akwai motsa jiki kala,kala da tausa, da Acupuncture duk suna taimakawa me ciwon baya.

Maganin ciwon baya mai tsanani

Ana bayyana ciwon baya a matsayin me tsanani idan ya kai ko kuma ya wuce watanni 3 ba tare da ya warke ba.

Karanta Wannan  Alamomin ciwon koda da abincin mai ciwon koda

Zai iya rika zuwa yana tafiya, kuma shima duk kusan abubuwan da muka zayyano a sama ne ke kawoshi.

Akwai abubuwan da Likitoci kwararru da suke kware a fannin ciwon baya suka bada shawarar yi dan maganin ciwon baya me tsanani.

Wasu daga cikinsu sune:

  • Motsa jiki, idan so samune likita ya gaya maka irin motsa jikin da ya kamata ka rika yi.
  • Samun nutsuwa, da yin abinda zai kwaranye damuwa.
  • Cin abinci me kyau, musamman wanda ba’a sarrafa ba yana taimakawa wajan maganin ciwon baya.
  • A daina shan taba, sigari idan ana yi, a kuma daina yin duk abinda ke karawa ciwon bayan tsanani.
  • Tausa na taimakawa ciwon baya me tsanani.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *