
A dazu ne muka ga Bidiyon diyar Tsohon shugaban kasa, Marigayi, Janar Muhammadu Buhari Watau Zahra Buhari tana ta kuka.
A yanzu kuma, Bidiyon mahaifiyarta, Hajiya A’isha Buhari ce ke kuka.
An ga A’isha Buhari na kuka ne yayin da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya je mata ta’aziyya.
A gobene dai za’a yi jana’izar gawar shugaba Buhari a mahaifarsa dake Daura.