APC ta rufe ofishinta na kasa domin rasuwar Buhari.

Mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Bukar Dalori, ya umarci a rufe hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja domin girmama marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi.
Umarnin ya na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Felix Morka, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta bukaci mambobin jam’iyyar da su yi amfani da wannan lokacin na zaman makoki na kasa wajen yin addu’a domin samun rahamar Allah ga marigayi shugaban.
“Kamar yadda mukaddashin shugaban jam’iyyarmu mai girma, Hon. Bukar Dalori ya umarta, za a rufe Hedikwatar Jam’iyyar ta Kasa tun daga yau Litinin, 14 ga Yuli, kuma za a bude ranar Alhamis, 17 ga Yuli, 2025.
“Muna kira ga mambobin jam’iyya da su yi amfani da wannan lokacin na makoki na kasa wajen yin addu’a domin samun rahamar Allah ga marigayi jagorarmu,”in ji sanarwar.