
Rahotanni sun tabbatar da cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zai karbi gawar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari a filin jirgin Katsina idan ta karaso daga landan.
A yanzu haka dai ana dakon jiran gawar tsohon shugaban kasar inda manyan mutane suka hallara dan halartar jana’izar tasa.