Friday, December 5
Shadow

Ji bayani dalla-dalla Abin da ya sa na fice daga PDP – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

A wata sanarwa da ya fitar mai kwanan watan ranar 14 ga watan Yulin 2025, Atiku Abubakar ya ce “ina sanar da jama’a ficewata daga jam’iyyar PDP ba tare da ɓata lokaci ba.”

“Ina son yin amfani da wannan damar na bayyana godiyata ga jam’iyyar ta PDP bisa irin damarmakin da ta ba ni: Na yi mataimakin shugaban ƙasa karo biyu a jam’iyyar sannan na yi takarar shugaban ƙsa karo biyu a PDP. A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar ta PDP, saboda haka akwai sosa rai ƙwarai dangane da ɗaukar wannan hukunci.” In ji Atiku.

Dangane kuma da dalilin da ya sa tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya bar jam’iyyar a wannan lokaci sanarwar ta ce:

Dole ne na raba gari da jam’iyyar a yanzu bisa la’akari da yadda PDP ta sauka daga harsashinta na asali da muka fata domin shi. Lallai abin da sosa rai ficewa daga cikinta bisa dogaro da yadda ba za mu daidaita ba da jam’iyyar.” In ji Atiku Abubakar.

Daga ƙarshe sanarwar ta yi wa jam’iyyar ta PDP da jagorancinta fatan alkairi.

A ranar 3 ga watan Yulin 2023 ne dai wasu gaggan ƴan hamayya a Najeriya suka sanar da dunƙulewarsu a jam’iyyar ADC domin yin haɗaka su ƙalubalanci ƙudirin shugaba Bola Tinubu na tazarce a 2027.

Karanta Wannan  Har Yanzu Akume Ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, Cewar Fadar Shugaban Ƙasa

Ƴan siyasar, ƙarƙashin jagorancin sanata David Mark, sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da Rotimi Amaechi da Rauf Argebesola da Malam Nasiru El- Rufai da dai sauran jiga-jigan ƴan siyasa daga kudu da arewacin ƙasar.

Irin wannan haɗaka ce dai a shekarar 2015 ta bai wa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari damar jagorancin ƙasar, sakamakon ƙalubalantar shugaban lokacin mai neman tazarce, Goodluck Ebele Jonathan a ƙrƙashin jam’iyyar APC.

To sai dai kamar sauran jam’iyyu, ƙulla alakar Atiku Abubakar da ADC ba tare da ya bar jam’iyyar ba ta ƙona wa jam’iyyar PDP rai, al’amarin da ya sa jam’iyyar ta nemi da tsohon mataimakin ya fice daga jam’iyyar ko kuma su hukunta shi.

PDP ta gargaɗi Atiku da muƙarrabansa

Tun dai bayan sanar da dunƙulewar da Atiku da wasu ƴan siyasa suka yi a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, jam’iyyar hamayya ta PDP ta nuna cewa ba ta lamunta da tsarin ba, kasancewar Atikun bai sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ba.

Karanta Wannan  Wallahi Da Yawan Mahajjatanmu Ba Su San Yadda Ake Dawafi Ba Duk Suna Kashe Makudan Kudade Su Zo Hajji, Wallahi Mun Sauka A Filin Jirgi A Jidda Wani Bafulatani Ya Ga Hoton Wata Balarabiya Kyakkyawa Sai Yake Tambaya Wannan Ita Ce 'Nana Aisha'?, Inda Sheik Gadon Kaya

A wata tattaunawa da BBC, shugaban jam’iyyar PDP na riƙo, Umar Damagum ya ce jam’iyya za ta hukunta duk wadda ya tafi zuwa haɗaka.

“AI mutanen da ke alƙanta kansu da ADC ɗin dama can su ne matsalar PDP, kuma lallai ne su futo su zaɓi ko PDP ko kuma ADC. Babu yadda za a yi mu bar su su zamar mana ƙadangaren bakin tulu,” kamar yadda Ibrahim Abdullahi ,mataimakin mai magana da yawun jam’iyyar ta PDP a Najeirya ya shaida wa BBC.

Da aka tambaye shi ko me zai ce dangane da yadda ministan Abuja, Nyesom Wike yake jam’iyyar PDP kuma a lokaci guda yana aiki ga jam’iyyar APC, sai ya ce:

“Ai su ne sanadiyyar tunzura Wike duk abubuwan da yake yi a jam’iyyar su ne ummul-aba-isi.”

Shi ma gwamnan jihar Bauchi Bala Muhamamd a tattaunawarsa da BBC, ya ce “ba zan bi sakarci ba” na bar jam’iyyar PDP na koma wata adda.”

Baya ga Atiku Abubakar, akwai ƙarin wasu jiga-jigan jam’iyyar ta PDP kamar Alhaji Sule Lamiɗo da Amabasada Aminu Wali da sanata Abdul Ningi da suka hallara a wurin taron haɗakar ba tare da ficewa daga jam’iyyarsu ta PDP ba.

Karanta Wannan  Addini Sauki Gareshi:Ko Tuntunbe ka yi zaka iya ajiye Azumi>>Inji Young Sheikh

Abin da ya sa PDP ke jin haushin ADC – Masani

Dangane da dalilin da ya sa jam’iyyun PDP ke takaicin alaƙar Atiku Abubakar da wasu ƴan ja’iyyar irin su tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, Malam Kabiru Sufi masanin siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami’a a kano wato CAS ya ce saɓanin haɗakar da aka saba gani wannan haɗakar ta ADC ta zo da wani sabon salo wanda bai zama lallai ya yi wa jam’iyyun da aka bari daɗi ba.

“A wannan karon ƴan jam’iyyun ne suka fito daga jam’iyyunsu suka shiga jam’iyyar da take da rijista, inda wasu ma ba su sanar da fita daga jam’iyyun nasu ba. Misali ƴan jam’iyyar PDP da dama an gan su a taron haɗakar kuma ba tare da sanar da ficewarsu daga jam’iyyar tasu ba.”

Masanin ya ƙara da cewa a baya an yi haɗaka iri-iri masu kama da wannan.

“Ko a jamhuriya ta biyu mun ga yadda jam’iyyu kan yi haɗaka domin ƙalubalantar jam’iyya mai mulki, inda ƴan jam’iyya kan shiga haɗakar ba tare da barin jam’iyyunsu ba. Misali za ka ga a tarayya ana haɗaka amma kuma a jihohi kowa na jam’iyyarsa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *