Tinubu ya naɗa ɗan tsohon shugaban ƙasa, IBB a matsayin shugaban Bankin Noma na Ƙasa.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), a matsayin Shugaban Bankin Noma na Ƙasa (BOA).
Sanarwar naɗin ta fito ne a ranar Juma’a ta bakin Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin yada labarai .
A cewar Onanuga, shugaban ƙasa ya amince da naɗin ne a yau Juma’a tare da wasu mutane guda bakwai.
“Wasu daga cikinsu za su yi aiki a matsayin shugabanni na hukumomin gwamnatin tarayya,” in ji shi.
A cewar sanarwar, Muhammad Babangida ya yi karatu a Jami’ar Turai da ke Montreux, Switzerland, inda ya samu digiri na farko a fannin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration) da kuma digirin digirgir (Master’s) a fannin Hulɗar Jama’a da Sadarwar Kasuwanci.