
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa, fitar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar daga cikinta bata damesu ba saboda sun san zai dawo.
Shugaban jam’iyyar na riko, Iliya Damagum ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace siyasa juyi juyi ce.
Yace suna da yakinin dawowar Atiku jam’iyyar tasu nan gaba.