Friday, December 5
Shadow

Ji yanda Rashin Buhari ya dakatar da shari’ar tsohon Gwamnan Adamawa, Murtaka Nyako da ake zargi da handamar Naira Biliyan 29

Rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo tsaiko a shari’ar da ake wa tsohon Gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako bisa zargin satar Naira Biliyan 29.

Ana shirin yon sulhu tsakanin gwamnatin tarayya a wajan kotu da Murtala Nyako amma sai mutuwar Buhari ta kawo tsaiko.

A ranar Juma’a ne ya kamata ace an ci aba da shari’ar ta Nyako amma ragin zuwan babban lauyan gwamnati, Prince Lateef Fagbemi (SAN) ya kawo tsaiko a shari’ar.

Dan haka ne mai shari’a Justice Peter Lifu ya dage shari’ar sai zuwa 25 ga watan Yuli kamin a ci gaba.

Kotun tace itama tana sane da kwanaki 7 na jimamin rasuwar Buhari da Gwamnatin tarayya ta ware.

Karanta Wannan  'Safiya ce mai wahala da kuma baƙin ciki' - Shugaban Isra'ila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *