Sunayen da Masoya ke amfani dasu na da yawa, ya danganta mace ce ko Namiji?
Kowane masoyi zai so ya fadawa Masoyinsa kalma me dadi da zata faranta masa rai ta koma kara musu shaukin juna.
Ga wasu jerin sunayen masoya da zaku so gayawa junanku.
Misali idan budurwar ka tace maka sweety, kai kuma kana iya ce mata Chakuleti.
Akwai irin su Honey ko Farin cikina.
Za kuma a iya kiran maaoyi da Madara, ko Burger.
Namiji yana so a kirashi da prince ita ma zata so ka mayar mata da princess.
Zaki iya ce masa Yarima, kai kuma ka kirata da gimbiya.
Idan kina son tsokanarsa, zaki iya ce masa dan ta matsisi, Kai kuma zaka iya ce mata lubiya.
Kana iya ce mata wutar lantarki ne.
Kana iya kiranta da Lollipop kema kina iya kiransa da hakan.
Kana iya kiranta da Kankana, ko Mangwaro.
Ke kuma kina iya kiransa da Rake ko Karas.
Kuna iya cewa juna Sugar.
Da dai sauransu, duk sunaye ne masu dadi dake nuna ana shaukin Juna.