Saturday, April 26
Shadow

Dalibar jami’ar Federal Polytechnic Bida, Jihar Naija me suna A’isha ta mutu a dakin Saurayinta me suna Akin wanda shima an sameshi ba rai

An samu dalibai biyu na jami’ar Federal Polytechnic  Bida, dake jihar Naija wanda masoya ne sun mutu a daki daya.

Dalibar me suna A’isha ta mutu ne a dakin saurayinta me suna Akin wanda shima an iskeshi ya mutu.

Kafar Sahara Reporters data ruwaito labarin tace an samesu duka bakunansu da kumfa wanda ake kyautata zaton guba ce suka sha suka mutu.

Saidai zuwa yanzu babu wani karin bayani kan lamarin amma ‘yansanda sun dauki gawarwakin zuwa mutuware.

Hukumar makarantar tasu ma taki tace uffan kan lamarin.

Karanta Wannan  Da Ɗumi-Ɗumi: Alhaji Obobo ya fara tattaki daga Ogun zuwa Kano, domin ziyartar mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, tare da Kaftin Ahmed Musa MON

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *