Friday, December 5
Shadow

ASUU ta ƙi amincewa da sauya sunan jami’ar Maiduguri da Tinubu ya yi don karrama Buhari

Reshen Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) na Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ya yi watsi da matakin gwamnatin tarayya na sauya sunan jami’ar zuwa sunan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Kungiyar ta soki wannan mataki tana mai cewa “yana da ɗauke da manufar siyasa” kuma “ cin mutunci ne ga tarihin jami’ar da aka kafa tun shekaru.”

Jaridar Leadership ta rawaito cewa shugaban ASUU, reshen UNIMAID, Dr. Abubakar Mshelia Saidu, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri wacce jaridar Leadership ta samu a ranar Lahadi, ya bayyana adawa ga wannan mataki.

Kungiyar ta bayyana cewa sauya sunan raini ne ga tarihin UNIMAID mai ɗimbin daraja kuma yana lalata mutuncin kimiyya da jami’ar ta gina tsawon shekaru.

Karanta Wannan  Mulkin Tinubu ya talauta masu kudi da yawa>>Inji Atiku

“Wannan mataki abin mamaki ne ƙwarai kuma yana ɓata tsarkin makarantar mu,” in ji sanarwar. “UNIMAID ba wai suna kawai bane—yana wakiltar shekaru da dama na ƙwarewar kimiyya, juriya, da muhimmancin ƙasa baki ɗaya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *