Yadda motar da ta yi karo da tawagar Gwamna Radda ta yi rugu-rugu

Wannan itace mota kirar Golf da ta yi karo gaba da gaba da motar Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda kan hanyar Daura zuwa Katsina. fatan Allah ya basu lafiya ya kiyaye faruwar hakan a gaba.
Rahotanni sun ce fasinjojin dake cikin motar kirar Golf sun samu karaya da raunuka. Sai dai Gwamnan jihar na Katsina, Radda bai ji wani mummunan rauni ba.

