
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa da bai ci zaben shekarar 2023 ba da tarihin Najeriya bai kammalu ba.
Ya bayyana hakane a yayin da yaje gaisuwar Basarake, Oba Sikiru Adetona na jihar Ogun.
Tinubu yace ya zama shugaban kasa ne saboda su da kuma Addu’ar da suka masa.