
rahotanni sun bayyana cewa, Kamfanin simintin BUA na shirin rage farashin simintinsa.
Hakan na zuwane daga bakin shugaban kamfanin, Abdulsamad BUA inda yacw hakan na da alaka da samun saukin canjin Naira da dala da kuma raguwar kudin samar da simintin.
Ya bayyana hakane a babban taron kamfanin na kasa AGM da aka yi a Abuja.
Yace a yanzu farashin dala ya doshi saukowa zuwa 1,500 akan kowace dala yace idan ya dawo zuwa 1,200 akan kowacw dala, za’a ga saukin farashin kaya sosai hadda siminti.