Friday, December 5
Shadow

Shekaruna 97 amma ban taba ganin irin gatan da shugaba Tinubu yawa gawar shugaba Buhari ba shiyasa zamu zabeshi a 2027>>Inji Sarkin Daura

Dalilan da su ka sanya za mu yi Tinubu a 2027- Sarkin Daura

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Sarkin Daura a Jihar Katsina, Umar Faruq-Umar, ya ce zai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya ya yi tazarce a 2027 saboda girmamawar da shugaban ya yi wa masarautar Daura da kuma Jihar Katsina ta hanyar yi wa wanda ya gada, tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, jana’izar ban-girma.

Sarkin ya bayyana goyon bayansa ne a fadarsa da ke Daura a ranar Asabar yayin da ya tarbi tawagar matan gwamnonin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Uwargidar Shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu.

A yayin ziyarar ta Remi Tinubu a fadar da, Sarkin, wanda ya gode wa shugaban kasa bisa girmamawar da ya nuna wajen jana’izar Buhari, ya tashi tsaye yana maimaita sunan shugaban ƙasa tare da bayyana goyon bayansa ga tazarce.

Karanta Wannan  Matashi me suna Abdullahi dan jihar Katsina da ya yi ridda ya koma Kirista ya fito ya godewa Allah inda yace da yana hanyar bata Amma yanzu Allah ya nuna masa hanyar gaskiya

Ya ce: “Na gode wa Shugaba Bola Tinubu, mutumin kirki da na shafe fiye da shekaru 30 tare da shi. Duniya za ta iya shaida abin da shugaban ya yi wa wannan jiha da masarautar Daura. Shekara ta 97, ban taɓa ganin jana’izar da aka yi da kima da daraja irin wacce Tinubu ya yi wa Muhammadu Buhari ba.

“Ya zo da kansa, ya kwashe kwanaki yana jimamin rasuwar tsohon shugaban, har hutu ya bayar a faɗin ƙasa don girmamawa, ya bayar da jirgin shugaban kasa don ɗaukar gawar, kuma aka kawo gawar aka binne ta a gaban shi. Yanzu kuma, ya turo Uwargidar Shugaba, Uwargidar Mataimakin Shugaba, da matan gwamnonin jihohi don yin ta’aziyya.

Karanta Wannan  Matar shugaban kasa,Remi Tinubu ta kashe Naira Miliyan Dari bakwai wajan yawon zuwa kasashen Duniya a cikin watanni 3 kacal

“Wannan girmamawa da aka nuna mana daga Shugaban Ƙasa ba za mu taɓa mantawa da ita ba; za mu rama hakan. Saboda haka a 2027, Tinubu za mu zaɓa,” in ji Sarkin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *