Friday, December 5
Shadow

Kuma Dai: Bayan Filayen da ya baiwa ‘ya’yansa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sake baiwa mahaifinsa da ‘yan uwansa maza da mata da abokai tarin filaye a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya Biwa mahaifinsa, Joshua Nlemanya Wike dan shekaru 90 fili a Abuja.

Rahoton yace Wike ya baiwa mahaifin nasa filinne a Guzape II wanda darajarsa ta kai ta Naira Miliyan 400.

Hakanan bayan mahaifinsa akwai ‘yan uwansa maza da mata da abokai da ya baiwa filayen a Abuja.

Hakan na zuwa ne kwanaki bayan da aka zargi Wike da baiwa ‘ya’yansa filaye a Abujan, zargin da ya karyata yace Atiku ne ke son bata masa suna.

Rahoton yace mutane 38 ne Wike ya baiwa ma’aikatansa yace a basu filaye, ma’aikatan da yawa sun yi mamakin wannan abu, kamar yanda peoplesgazette ta ruwaito.

Karanta Wannan  Babu irin muguntar da Buhari bai shiryawa Tinubu ba dan ya fadi zaben 2023 amma da yake Allah na sonshi, ya tsallake>>Inji Ministan Abuja Wike

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *