
Majalisar Dattijai ta Najeriya ta bayyana cewa, Wasan Kwaikwayo ne ya kai sanata Natasha Akpoti majalisar a jiya talata har take kokaron shiga ciki.
Majalisar ta bayyana hakane ta bakin me magana da yawuntaz Sanata Yemi Adaramodu a hirar da aka yi dashi.
Yace ko da akwai hukuncin kotu, ba sanata Natasha Akpoti bace da kanta zata zartar dashi ba.
Yace akwai wakilin kotu da ya kamata ya kaiwa majalisar takardar hukuncin da ootun ta yi.
A jiya talata ne dai Sanata Natasha Akpoti ta yi yunkurin shiga majalisar da karfin tsiya amma abin ya faskara.