
Wasu Sojojin da aka aika samar da tsaro na tsawon wata daya amma aka basu abinci dan kadan lamarin ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta bayan da suka dauki Bidiyo suka yada.
Sun ce abincin ma sai da aka karbi kudi a hannunsu kowa dubu 60 amma aka kawo musu wannan abincin dan kadan.
Sunce kifi 5 aka kai musu da sai bokitin fenti na Garin Kwaki da wake, Doya guda 4, Lita daya ta man ja, karamin buhun shinkafa, Semolina me girman 10kg.