
Daga Muhammad Kwairi Waziri
Wani matashi a unguwar Nasarawa da ke Bauchi ya janyo hankalin jama’a bayan ya hau saman karfen sabis yana ƙoƙarin janyo kulawar jama’a da gwamnati. Matashin ya bayyana cewa ba zai sauko ba sai dai in Dan Gwamna Bauchi, Shamsudeen Bala Mohammed, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata a 2027.
Lamarin ya janyo ɗimbin mutane da suka taru domin kallo, yayin da jami’an tsaro da na hukumar bada agajin gaggawa suka isa wajen domin shawo kansa.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana matakin a matsayin “dabarar jawo hankali” yayin da wasu ke kallon sa a matsayin “alamar gajiya da rashin sauraron muradun matasa”.