Friday, December 5
Shadow

‘Jam’iyyarmu ta APC na fuskantar barazanar faɗuwa a 2027’>>Inji Adamu Garba, ji dalilinsa

Wani jigo a jam’iyyar APC mai muki a Najeriya wanda kuma ya nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar a baya, ya bayyana wa BBC cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsu ta APC na fuskantar babbar barazana a zaɓe mai zuwa.

Alhaji Adamu Garba, ya ce makusantan shugaban ƙasar ba sa fada masa gaskiya kan ainihin abin da ke faruwa musamman a arewacin ƙasar, yana gargaɗin cewa hakan zai iya jefa gwamnatin cikin haɗari.

Ya kara da cewa hadakar ‘yan hamayya ta ADC na iya zamar wa APC kadangaren bakin tulu a zaɓe mai zuwa, musamman bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

Ya ce idan aka lura tsarin da aka bi wajen kirkiro APC tun ainahi, jam’iyyar ta samu mafi rinjayen kuri’unta daga arewa ne har ta kafa gwamnati a 2015.

”Saboda mu arewaci a wannan lokacin mun samar da kuri’u miliyan 12 da ‘yan kai, yayin da kudu ta bayar da kuri’un da ba su fi miliyan uku da wani abu ba,” in ji shi.

‘Jam’iyyar haɗaka barazana ce a gare mu’

Ya kara da cewa : ”Kuma wanda ya kawo wadannan kuri’u shugaba ne marigayi Muhammadu Buhari saboda haka tafiyarsa ta nuna cewa mutane da yawa da suka bi shi tun 2002 da ya fara kamfe har zuwa yanzu ina ne makomarsu?”

Karanta Wannan  Sanata Ali Ndume yayi Allah wadai da kama Hamdiya Sidi saboda kokawa da ta yi da kisan da 'yan Bìndìgà suke yi a jihar Sokoto

”Shi ya sa nake hango mana a kan cewa idan ba mu kawo sababbin tsari da muka jawo waɗannan mutanen suka ci gaba da tafiya da APC ba, za mu fuskanci abin kunya a zabe mai zuwa na 2027,” ya ce.

Dangane da haɗakar da masu hamayya ke yi ta gamgamko a jam’iyyar ADC, ko hakan na zamar wa APC wata barazana idan aka tafi a haka? Sai tsohon mai neman takarar ya ce tabbas akwai barazana.

Ya ce: ”To ai ta bayyana sosai za ka ga mafi akasarin ministocin da suke tare da Buhari a gwamnatinsa a wancan lokacin gaba daya sun koma ADC. Wadanda ba su koma ba ma suna tattaunawa suna komawa.”

”Sannan idan ka dubi tattalin arziki ya tabarbare, mutane tsadar rayuwa ta yi yawa. Kowa in ya daga hannu sai ya nuna ai gwamnati ce.

Karanta Wannan  'Yan Australia sun shiga sabuwar shekara

Alhaji Garba ya yi nuni da yadda ya ce wasu daga cikin manyan jam’iyyar na nuna cewa babu wata matsala.

”Idan suka fito suna bayani nunawa suke kamar babu komai, komai lafiya kalau.

Kuma idan ka zauna da su kuna hira, duk wanda ka je ka zauna da shi sai ma ya gaya maka ya ma fi ka fahimtar matsalar da yake ciki.” In ji shi.

‘APC ba ta son gaskiya’

Jigon ya kara da cewa : ”Kuma mafi akasarinsu ba ma ‘yan arewa ba ne ba su san zaben arewa ba, ba su san tafiyar arewa ba.

”Su sun dauka kamar irin tafiya ce ta su ta kudu wadda ake bin shugaba kawai a makance.

”Mu arewa yadda tsarinmu yake, tsari ne wanda suke bin mutum saboda yarda da aminci,” ya ce.

Alhaji Garba ya yi tsokaci da yadda ake kallon duk wanda ya fito ya fadi gaskiya a jam’iyyar tasu kamar bai san abin da yake ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon Lefen Kece Raini da Rarara yawa A'isha Humaira da mutane ke cewa Almubazzaranci ne

Ya ce irin wadannan kalmomin ake zuwa ana gaya wa shugaban kasa a kan komai na tafiya sannan mu kuma da muke arewa mun san tabarbarewa komai yake yi.

”Ba yanda za a yi mu zauna mu ga abu na tabarbarewa mu yi shiru ta zo ta baci daga baya a ce ba mu fito mun fada ba,” in ji shi.

Dangane da matakan da za a bi a jam’iyyar ta APC a gyara tafiyarta, Alhaji Graba ya bayar da shawara:

”Ya kamata a tsara jam’iyyar a nemi shugaba amintacce kuma nagartacce wanda idan ya yi magana ana amincewa da shi kuma an san shi da adalci duk lokacin da ya samu dama.

”Zai iya cewa ya yarda zai iya cewa bai yarda ba, ba tare da ya ja mutane ya rudi mutane, ya yaudari mutane ba.” Ya ce.

Ya kara da cewa, ”dole sai an gyara mu zo mu fita da kunya wannan abin shi ne muke gudun kada ya faru,” in ji Alhaji Garba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *