
Wata mata me suna Hadiza Mamuda ‘yar kimanin shekaru 35 ta make mijinta da itace ya mutu a kauyen Garin Abba dake karamar hukumar Fika ta jihar Yobe.
Lamarin ya farune yayin da muhawara ta yi zafi tsakaninsu akan abinci.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kama matar inda ake bincike kuma za’a gurfanar da ita a gaban kotu.
Yace mijin na da mata biyu kuma ya mutu ya bar yara 5.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Emmanuel Ado ya tabbatar da faruwar lamarin inda yayi kira ga shuwagabannin al’umma da malamai su rika fadakar da mutane kan zamantakewar rayuwa.