
Rahotanni da muke samu na cewa, Allah yawa Me martaba Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello rasuwa.
Ya rasu yau, Juma’a a Abuja bayan jinya.
Hutudole ya fahimci cewa, Sarkin ya rasu yana da shekaru 71 a Duniya.
Ya zama sarki ne a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2015 bayan rasuwar mahaifinsa.
Kakakin Gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Idis ya tabbatar da rasuwar Sarkin inda ya mika sakon ta’aziyya.