
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Ministan Wutar Lantarki ya sanar dashi cewa an samu ingancin wutar.
Shugaban ya bayyana hakane a yayin ganawa da wasu ‘yan kasuwa masu zuba hannun jari.
Shugaban yace Najeriya bata kai inda take son kaiwa ba game da karfin wutar lantarki.
Yace kuma wutar tana da muhimmanci wajan ci gaban kowane bangare na rayuwar Al’ummah.