
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yayi kokari a yanzu duk Talauci Talala yana samu ya ci shinkafa a gidansa.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Daniel Bwala a hirarsa da DW.
Bwala yace Tsare-tsare gwamnatin Tinubu sun sa Shinkafa ta wadata a kowane mataki na ‘yan Najeriya.
Yace kuma sun samarwa mata masu ciki da basa iya haihuwa an musu aiki kyauta hakanan akwai magungunan da suka rika bayarwa kyauta