Wednesday, September 23
Shadow

Rashin Adalci Ne A Bawa Ƴan Kwallo Milyan 150, Da Gidaje Kowannen Su Cikin Wata Ɗaya, Amma Ɗan Sanda Ya Shekara 35 A Ba Shi Milyan Biyu, Inji Sowore

Rashin Adalci Ne A Bawa Ƴan Kwallo Milyan 150, Da Gidaje Kowannen Su Cikin Wata Ɗaya, Amma Ɗan Sanda Ya Shekara 35 A Ba Shi Milyan Biyu, Inji Sowore.

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Omoyele Sowore, ɗan gwagwarmaya kuma mai kare haƙƙin ɗan adam, ya bayyana rashin adalci a tsarin albashi da lada a Najeriya, yana mai cewa abin takaici ne yadda ake fifita ‘yan wasa fiye da ma’aikatan tsaro.

A cewarsa: “Rashin adalci ne tsantsa, ‘yan kwallo su yi wasa a cikin wata ɗaya a ba su Naira miliyan 150 da gidaje kowanne, amma ɗan sanda ya shekara 35 yana aiki ya samu Naira miliyan 2 kawai ba tare da wani tausayi ba.”

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Mutanen Shafa Wali sukawa Hamisu Breaker kyautar sama da Naira Miliyan 7

Sowore ya ce irin wannan bambanci yana nuna rashin daraja da ƙasa ke yi wa waɗanda ke sadaukar da rayukansu don tabbatar da tsaro da zaman lafiya. Ya bukaci a sake duba tsarin biyan haƙƙin ma’aikata a ƙasar.

Me zaku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *