
Gwamnoni 18 na Arewacin Najeriya sun hada kai inda suka ce basa tare da masu sukar Tinubu suna cewa ya ware yankin Arewa baya ma yankin aiki
Gwamnonin sun bayyana hakane ta bakin shugaban kungiyarsu, Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya.
Gwamna Yahya ya fada a yayi jawabi wajan taro a Arewa House dake Kaduna wajan taro tsakanin shuwagabanni da Talakawa na kwanaki biyu
Gwamnan yace lallai akwai matsin rayuwa wanda suka samo Asali daga cire tallafin man fetur da na dala. Yace amma fa ci gaban ma akwaishi.
Ya kawo misalai na Gyaran Titin Abuja zuwa kaduna, da Kano.
Da hakar man fetur a Kolmani da dai sauransu.