
Jam’iyyar SDP me doki inda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya koma ta karyata labarin da yayi yawo sosai cewa, ta dakatar da El-Rufai tsawon shekaru 30.
Kakakin jam’iyyar a jihar Kaduna, Hon. Darius Kurah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai inda ya bukaci mutane su yi watsi da wanan magana.
Yace wanda aka ce ya fitar da labarin me suna, Araba Rufus Aiyenigba wanda aka ce kakakin jam’iyyar SDP ne karyane bashine kakakin jam’iyyar SDP na kasa ba.
Yace kuma abinda ake yadawa cewa, wai El-Rufai na munafurtar jam’iyyar SDP shima ba gaskiya bane.