
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada lumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon shugaban hukumar kwana-kwana masu kashe Gobara ta kasa.
Lumode zai fara aiki ne ranar August 14, 2025 a matsayin sabon shugaban hukumar.
Hakan na zuwane yayin da shugaban hukumar na yanzu, Engr. Abdulganiyu Jaji ke shirin zauka ya ajiye aiki bayan kaiwa shekarun ritaya watau shekaru 60.