Friday, July 17
Shadow

Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle yace Sojan Ruwa da ya tare Nyesom Wike bai aikata laifin komai ba

Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa, sojan ruwa, A. Yerima da ya tare Ministan babban birnin tarayya, Abuja Nyesom Wike bai aikata laifin komai ba.

Minista Bello Matawalle ya bayyana cewa sojan na bakin aikinshi ne kuma yana bin umarnin me gidansa ne.

Bello Matawalle ya bayyana hakane a hirar da aka gudanar dashi a gidan Talabijin na DCL Hausa.

Ya kuma kara da cewa, Wike yayi hattara dan kuwa wulakanta sojan da yayi kamar ya wulakanta shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne.

Karanta Wannan  Kamfanin DSTV da sauran tashoshi na Tauraron dan Adam sun tafka asarar Dala Miliyan $158.19 saboda 'yan Najeriya da yawa yanzu sun daina saka kati saboda matsin tattalin arziki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *