
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan kasuwar Man fetur sun rage farashin man fetur dinsu inda suke sayar dashi a farashi kasa da yanda matatar man Dangote ke sayarwa.
Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Dangoten yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya hana shigo da man fetur daga kasashen waje.
Jaridar Punchng ta ruwaito cewa, ‘yan kasuwar na sayar da man a farashin 860 akan kowace lita yayin da Dangote kuma ke sayarwa akan 865 zuwa 875 akan kowace lita.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ta IPMAN, Chinedu Ukadike ya tabbatar da rage farashin inda yace hakan na nuna kyawun kasuwa.
Yace yana kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kada ya saurari kiran da Dangote ke yi na cewa ya hada shigo da man fetur din daga kasashen waje.