Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyon yanda aka yiwa su Mansurah Isa Ba daidai ba a wajan taron siyasa hadda cire kaya a bainar Jama’a

Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana yanda aka wulakantasu a wajan taron siyasa na Sanata Barau I Jibrin.

Mansurah Isah a wani Bidiyo data wallafa a shafinta na sada zumunta ta bayar da labarin yanda aka gayyacesu wajan taron siyasar amma da suka je daya daga cikin jami’an tsaron yace fuskar daya daga cikinsu bata mai ba dan haka ya hanasu shiga.

Tace saboda cin mutunci hadda tubewa wata kaya a bainar Jama’a.

Mansurah ta nemi da sanata Barau I Jibrin ya kwato musu hakkinsu.

Kalli Bidiyon anan

A wani Bidiyo da ta sake wallafawa kuma, Mansurah Isah tace Barau Jibrin ya mata Alkawarin daukar mataki da kwato mata hakkinta ita da sauran abokan tafiyarta.

Karanta Wannan  Kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya ta lashe kofin Kwallon Kwando na mata na Afrika

Mansurah ta bayyana godiyarta da Farin ciki kan kulawar Sanatan.

Kalli Dayan Bidiyon anan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *