
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya zata kara farashin man fetur nan da 1 ga watan Janairu na shekarar 2026.
Hakan na kunshene a cikin sabuwar dokar haraji wadda aka zartas a kwanakin baya.
Dokar ta tanadi kara harajin kaso 5.0 cikin 100 akan man fetur wanda aka tace a gida Najeriya da kuma wanda aka shigo dashi daga kasashen waje.
Saidai wasu masu sharhi na cewa hakan bai dace ba lura da yanda a yanzu haka Talaka ke fama da kansa inaga an kara farashin man fetur?