
Kungiyar dake ikirarin kare hakkin Musulmai a Najeriya, MURIC ta bukaci Gwamnatin tarayya ta gina Kotunan shari’ar Musulunci a kowace jiha dake kasarnan.
Kungiyar tace dokar da ake amfani da ita babu adalci a ciki kuma akwai wasu sassa na kasarnan da babu kotunan Shari’a shiyasa take gabatar da wannan bukata.
Kungiyar tace dan hakane take bukatar gwamnatin tarayya kamar yanda aka gina manyan kotunan gwamnatin tarayya a kowace jiha to itama kotun shari’ar Musulunci a ginata a kowace jihar.
Shugaban kungiyar, Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.