
Hukumomi a jihar Katsina sun kama matashi me suna Anas Muhammad Game saboda yayi zanga-zanga kan matsalar tsaron dake damun jihar.
An kamashi ne kwanaki 6 da suka gabata a wajan zanga-zangar lumana ta nuna rashin jin dadin matsalar tsaron dake damun jihar.
Tun wancan lokacin dai Muhammad Game ke tsare ba tare da Beli ba.
Da yawa sun hau kafafen sada zumunta inda suke Allah wadai da ci gaba da tsareshi da neman a sakeshi da gaggawa.