ABIN A YABA: Wani Hakimi A Jihar Bauchi Ya Siyo Masara Ya Karya Farashinta Daga Naira 700 Zuwa 450 Domin Saukakawa Mabukata.

Wani bawan Allah Hakimin kasar Ciroma ta Masarautan Misau dake jihar Bauchi, Alh Amadun Amadu ne ya karya farashin masara daga naira 700 da ake siyarwa a kasuwa zuwa naira 450.
Hakimin ya siyo masarar ce da kudin sa domin saukaka mabukata su siya cikin farashi mai sauki.
Ana siyar da masarar ne a kofar gidansa, kuma ya ce daga nan har zuwa wata guda za a cigaba da kawo masarar ana siyarwa da mabukata.
Wace fata za ku yi wa wannan bawan Allah Alh Amadun Amadu?
Daga Mohammed Sale Gariyo Misau