
Hadimin Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party, Peter Obi, me suna Valentine Obienyem ya musanta cewa Ogan nasa ya shirya yiwa shugaba Tinubu juyin Mulki.
Ya zargi cewa, Wani me suna Arabambi ne ya kaiwa jami’an tsaro korafi akan Peter Obi da sauran wasu mutane irin su shugaban kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajaero, da sanata Victor Umeh da ‘yar majalisar wakilai, Nenadi Usman.
Valentine yayi kiran a gudanar da bincike sannan a kama wanda yayi wannan yarfen dan a hukuntashi.