Friday, December 5
Shadow

Ana cece-kuce tsakanin Gwamnan jihar Naija da Gwamnatin tarayya kan dakatar da gidan Rediyo

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma na Najeriya, Muhammad Idris Malagi ya buƙaci kowane ɓangare ya mayar da kubensa kan batun rufe gidan rediyon Badegi FM da ke birnin Minna a jihar Neja.

Ministan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Rabiu Ibrahim ya fitar, inda a ciki ya ce hukumar kafafen watsa labarai ta Najeriya wato NBC na da hanyoyin shiga tsakani idan aka samu irin wannan matsalar.

Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na jihar a ranar 1 ga watan Agusta.

Karanta Wannan  Nima ina goyon bayan a saki Nnamdi Kanu>>Inji Atiku Abubakar

Gwamnan ya zargi gidan rediyon ya karya dokokin watsa labarai, da kuma tunzura mutane a kan gwamnatin jihar.

“Duk da cewa mun fahimci abin da gwamnatin ke zargi, ma’aikatar watsa labarai na so a fahimci cewa Hukumar NBC ce ke da hurumin dakatar da lasisin gidan rediyo Gwamnatin Neja ba, kamar doka ta tanada.

“Don haka ne ma’aikatar ke kira ga gwamnatin jihar Neja da ta kai ƙorafinta ga NBC kan gidan rediyon NBC bisa zargin “karya doka” da take yi wa gidan rediyon.”

A ƙarshe ministan ya yi kira da a bi lamarin a hankali, inda ya tabbatar da cewa NBC za ta yi aikin da ya dace domin tabbatar da sasanci kan lamarin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda China ta yi Robot 'yan kwallo, kalli yanda suke buga kwallon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *