
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya roki ‘yan arewa da su sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027.
Yayi wannan rokone a yayin wani taro da ya shirya na tsaffin ‘yan majalisar tarayya a Abuja.
Ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu Tinibu ba shugaban kudancin Najeriya bane kadai, shugaba ne na kowanne yanki.
Yace ko dan Tinubu ya kammala ayyukan ci gaban da ya ke yi a Arewa, ya kamata ace ‘yan Arewan su sake zabensa.