
ABIN A YABA: Ya Tara Marayu Sama Da 200 Ya Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa Tare Da Su, Inda Ya Yi Wa Kowannensu Dinki
…samun matashi irin Hon. Muhammad Sulai Yaro abu ne mai wuya
Tabbas samun matashi kamar Hon Muhammed Sulai Yaro wanda aka nada shi a matsayin Dan Gatan Girei abu ne da kamar wuya, matashi ne da ya mayar da hankalin sa kan takalawa.
A jiya ne dai ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa, inda ya debi yara marayu sama da dari biyu ya yi musu sabon dinki, kuma ya hada musu liyafa, har saida ya zubar da hawaye a wajen.
Haka kuma ya yi musu alkawari zai ci gaba da tallafa musu har karshen rayuwar su.
Wace fata za ku yi masa?
Daga Hon Ishaq B Aliyu