Friday, December 5
Shadow

Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC

Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua wanda ya wakilci mazabar Katsina ta tsakiya a majalisar tarayya ya bayyana cewa, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.

A takardar da ya aikewa da mazabarsa ranar 28 ga watan Yuli, Tsohon Dan majalisar ya bayyana cewa, tsare-tsaren jam’iyyar APC sun jefa al’umma cikin halin kaka nika yi.

Yace da gaskene kalaman Malam Nasir El-Rufa’i da yace gwamnatin Tinubu ta koma ‘yan Bindigar birni.

Abubakar Sadiq ‘Yar’Adua wanda yayi takarar gwamnan jihar Katsina a zaben 2023 yace Gwamnatin Tinubu na biyewa Turawa ne wanda burinsu tara Duniya yana jefa ‘yan Najeriya a wahala.

Yace yana fatan shi da mabiyansa zasu koma jam’iyyar ADC nan gaba kadan

Karanta Wannan  Allah Sarki kalli bidiyon yawabi me sosa Zuciya na Sheik Makari akan Kananan yaran da gwamnatin Tinubu ta kai Kotu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *