
Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu da Matar Ministan tsaro sun baiwa Tauraruwar Tiktok, Rahama Sa’idu Aikin koyarwa da yara mata tsafta bayan jinin haila da nuna muhimmancin Ilimi garesu da yanda kuma zasu inganta rayuwarsu.
Tun da farko dai an ga Rahama Saidu a titi tana wakar Omologo tana shelar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Daga baya kuma an ga yanda aka shirya wani gagarumin taro inda aka ga Rahama ta gabatar da jawabi.
Daga cikin shirin hadda rabawa yara mata Pads, da koya musu yanda ake amfani dashi.
A wani Bidiyon an ga Rahama tare da mahaifiyarta suna rawa.
Kasancewar Rahama Saidu korarta aka yi daga makarantar koyan aikin jinya, wasu sun fito sun fara sukar wannan aiki da matar shugaban kasa ta bata na karfafawa yara mata gwiwa kan karatu.
Saidai Tuni wasu na hannun damar Rahama Saidu suka fito suka kareta da fadin cewa yanzu haka tana makaranta.