Rahotanni da muke samu na cewa wata tankar dakon man fetur ta sake fashewa a jihar Jigawa.
Lamarin ya farune a kan iyakar jihar ta Jigawa da Kano.
Kakakin hukumar kwana-kwana ta jihar, Aliyu M. A. Ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar laraba.
Yace lamarin ya farune a Tsaida, Kwanar Kalle inda yace suna samun bayanan tashin gobarar suka garzaya inda lamarin ya faru kuma suka kasheta.
Hakan na zuwane wata daya bayan da aka samu tashin gobarar motar dakon man fetur wadda ta kashe mutane akalla 170 a jihar.