
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Amurka na shirin kakabawa kasashen Duniya sabuwar doka ta shiga kasarta.
Kasashen da wannan sabuwar dokar zata shafa sune kasashen da basu da cikakkun bayanai na ‘yan kasarsu da kuma wadanda ‘yan kasarsu ke yawan zuwa Amurka basa komawa kasashen su na haihuwa.
Yawanci wadanda abin zai shafa sune masu zuwa Amurka dan yawon shakatawa ko kasuwanci.
Dokar tace za’a bukaci mutane su rika ajiye dala $15,000, kwatankwacin Naira Miliyan 22 kenan, idan sun je Amurka sun ki dawowa gida Najeriya ko kasashensu na Asali, za’a rike kudin, amma idan sun dawo gida, za’a mayar musu da kudadensu.
Badai a bayyana sunayen kasashen da lamarin zai shafa ba amma masu sharhi akan al’amuran yau da kullun sun yi ittifakin akwai ‘yan Najeriya a ciki.