Saturday, April 11
Shadow

Masu son zama shugaban kasa sun yi yawa a ADC>>Inji Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jigawa, Malam Sule Lamido yace masu son zama shugaban kasa, sun yi yawa a jam’iyyar ADC.

Sule Lamido ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.

Sule Lamido wanda yana daga cikin wadanda suka halarci taron farko na hadakar ‘yan Adawa da suka zabi APC a matsayin jam’iyyar su, yace ba zai bar PDP zuwa karamar jam’iyya ba.

Yace yana baiwa masu son shugabanci a jam’iyyar ta ADC dasu natsu su zama cewa sun samu alkibla da hafin kai.

Akwai Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da duka suka bayyana son tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta ADC.

Karanta Wannan  Ba ruwana, Ya tsyani babana Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, inji Dan tsohon Gwamnan Kaduna Bello El-Rufai bayan da aka yi kira ya dauki mataki kan batan dan fafutuka na jihar Jigawa, Abiyo Roni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *