Friday, December 5
Shadow

Akwai yiyuwar Najeriya zata tarwatse kamin shekarar 2027>>Inji Nwodo

Tsohon Ministan yada labarai kuma tsohon shugaban kungiyar kare muradun Inyamurai, Chief John Nnia Nwodo yayi gargadin Najeriya na iya tarwatsewa kamin shekarar 2027.

Ya bayyana hakane a Abuja wajan kaddamar da wani littafin a dakin taro na Shehu Musa ‘Yar’adua ranar Laraba.

Nwodo yace tsarin da ake kai ba zai kai Najeriya ga ci ba, yace dole a canja fasalin kasarnan.

Ya bayyana cewa a canja kundin tsarin mulki kowane yanki a bashi dama ya rika cin gashin kansa yana biyan gwamnatin tarayya haraji.

Yace amma idan ba haka ba, wasu yankin ba zasu yi zabe ba sannan wasu zasu nemi ballewa daga Najeriya.

Karanta Wannan  Wani makiyin Addinin Musulunci ya kona Qur'ani a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *